Aƙalla ƴan Boko Haram da ISWAP su 6 ne suka rasa rayukansu a sakamakon tashin wani bom da suka yiwa sojoji tarko dashi, sai dai maimakon ya tashi da sojojin sai ya tashi akan mayaƙan na Boko Haram.
Jaridar Daily Nigerian Hausa itace ta rawaito cewa majiyoyin tsaro sun bayyana yadda ƴan ta'addan suka haɗu da ajalin su a ranar Alhamis, a kan hanyar su ta dawowa da ga kai wasu hare-hare a kan hanyar ƙauyen Nguma da ke Ƙaramar Hukumar Biu ta jihar Borno.
Wasu rahotanni sun ce ƴan ta'addan sun fito a motoci Masu ɗaukar jigida guda 3 da babura ɗaya a hanyar su ta dawowa da ga Sabongari da Multe, sai mota ɗaya ta taka bam ɗin. Wanda kuwa nan take bom din ya kashe shida daga cikin su inda kuma wasu daga cikin su suka ji munanan raunuka.
Rahotannin sun ce ƴan ta'addan da su ka rayu sun huce haushin su a kan wani bafilatani, inda su ka kashe shi da matar sa da kuma ɗan sa. Sai dai kuma ba'a bayyana adadin waɗanda suka ji raunuka ba, kafin jami'an tsaron soji suzo wajen duk sun gudu.
Cikin kwanakin nan dai hare-haren mayaƙan Boko Haram da ISWAP sai ƙara tsamari yake yi, ko a satin da ya gabata ma sai da ISWAP suka kai hari a garin Ndamari jim kaɗan bayan zuwan shugaban majalisar ɗinkin duniya, Antonio Guttrez.