Mahukuntan ƙasar Saudiyya, sun cafke a ƙalla mutane 20, wanda aka kama su suna ɗaga hotunan ɗan takarar shugaban ƙasa a Najeriya wato Bola Ahmad Tinubu da sauran wasu Ƴan siyasan Najeriya a gaban ɗakin Ka'aba, hukumomin sun bayyana cewa za'a hukuntasu daidai da laifin da suka aikata.
Majiyar ta cigaba da cewa a yanzu haka suna hannun mahukunta ƙasar, ƙarƙashin kulawar askarawa domin gurfanar dasu gaban kotu tare da yanke masu hukunci dai-dai da abinda suka aikata, majiyar kuma ta cigaba da cewa babu shakka zasu kwashi kashin su a hannu.
Majiyar mu ta kuma jiyo cewa, hukumomin sunce sun baza su amince da ire-iren waɗannan abubuwan da ƴan Najeriya suke yi ba, domin yin wani abu na daban a cikin ƙasar su ba, domin kuwa wannan sabon wani abu ne dasu ba susan da shi ba, kuma ba zasu amince ba.
Ƴan Najeriya ma na ta yin ƙorafi tare da yin Allah wadai game da irin abubuwan da aka ga wasu mutane suna yi a ƙasar ta Saudiyya wanda ake ganin yin hakan zubarwa da Najeriya mutunci ne a idon duniya, da kuma nuna rashin kishin ƙasar.
Sai dai wannan hukuncin da mahukunta ƙasar Saudiyya suka ɗauka yayiwa ƴan Najeriya daɗi, kuma suna fatan za'a hukunta su daidai da abinda suka aikata domin hakan ya zama izina ga sauran al'umma Waɗanan suke so su aikata hakan anan gaba.