Sassan Jikin Mace 5 Da Suka Fi Jan Hankalin Maza



Abubuwan da suke jan hankali da birge namiji yasha bamban da na wasu mazan. Kusan kowane namiji akwai abinda yafi birge shi da jan hankalin sa a jikin mace. Maza suna sha'awar ganin wasu sassan jikin mace wanda yake birge su kuma yasa su sha'awa har ya ja hankalin su gareta.


A cikin wannan rubutu na musamman, zamu kawo muku wasu abubuwa 5 daga cikin sifofin jikin mace da yake birge maza. Ga dai abubuwan a taiƙace kamar haka;


(1) Ƙirjin Mace, Nono (Breast)

Da wuya ka samu namiji wanda zai ce Nono a jikin mace baya birge shi. Duk namiji koda tsoho ne babu abinda yafi tayar masa da hankali a jikin mace da ya wuce Ƙirjin ta. Sai dai kusan kowane namiji akwai irin kalar Nono da yake so, wani na son ganin manya, wani kuwa yafi son tsaka-tsaki masu tsayi, wani kuma yafi son saffa-saffa gajeru.

 

Ƙirjin mace musamman budurwa yana ɗaya daga cikin abinda ke ƙara mata kyau kuma ya ƙara mata kwarjini a wajen maza. Shiyasa wasu ƴan matan zakaga suna yin ado da ƙirjin su domin jawo hankalin maza, musamman idan mace tanada su masu girma da tsayi. Su matan sun san wannan.


(2) Mazaunai, Ƙugu (hips)

Bugu da ƙari, wani sassa na jikin mace da yafi birge maza shine mazaunan ta, wato hips. Bisa wani binciken da masana suka gudanar, mafi yawan maza abinda ke tayar da hankalin su zuwa ga mace shine mazaunan ta. Domin yana ɗaya daga cikin abinda ke motsa sha'awa ga namiji idan yaga hips ɗin ta.


 Mata da yawa suna amfani da mazaunan su domin jawo hankalin maza zuwa garesu. Wasu mazan babu wani abu da ya fi tayar musu da sha'awar son jima'i sai sunga mace mai kyaun mazaunai. Shiyasa duk rashin kyaun fuskar mace indai tanada mazaunai zaka samu maza suna kai komo a wajen ta.


(3) Gashi (Hair)

 Yawancin maza suna sha'awar ganin gashin mata sosai. Yawancin samari suna alfahari da ganin gashin budurwar su ko matan da suke aure. Maza da yawa suna burin ganin gashin kan mace mai tsayi cikin gyara. 


Sannan kuma suna son sha'awar ganin gashi mai laushi da sheƙi, hakan yana ƙara saka musu nishaɗi da ƙarin soyayya ga macen da take da wannan gashin. Domin gashin kan mace yana taka muhimmiyar rawa a zukatan maza da yawa a duniya. 


(4) Idanu (Eye Candy)

Wani Abu kuma da shima yake birge maza a sassan jikin mace shine idanun ta, domin maza da yawa suna son ganin mace mai kyawawan idanu. Wani namijin babu abinda ke jan hankalin sa zuwa ga mace sai idanun ta. 


Ido yana da mahimmanci, kuma kalmar "Ƙauna a farkon haɗuwa" yana yiwuwa ne kawai lokacin da idanunku biyu suka haɗu da juna a karon farko. 


(5) Ƙafa (Leg)

Abu na ƙarshe a wannan rubutun shine, Ƙafa: Ƙafafun mata na ɗaya daga cikin abubuwan da ke jawo hankalin namiji zuwa ga mace. Ƙafafu masu kyau, musamman masu tsafta da kyaun gani, za su iya kasancewa abin sha'awa ne ganin su. Sai dai wasu mata rashin kula da ƙafafun nasu tare da tsaftace su yake korar maza daga wajen su.


Wasu matan sunfi ɓata lokaci wajen kulawa da tsaftace fuskokin su sai kuma su bar ƙafafun su ba tare da sun gyara su ba. A tunanin su fuska ce kawai abinda namiji zai gani yazo wajen su. Wani namijin kawai ƙafar ki ce zata birgeshi yazo wajen ki.


Wannan sune kaɗan daga cikin abubuwan dake jawo hankalin namiji zuwa ga mace. Abubuwan suna da yawa amma baza mu iya kawo muku su a rubutun ba, sai nan gaba za ku ji mu da wasu.

Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post