Rundunar haɗin gwiwa ta sojin Najeriya da Kamaru sun hallaka ƴan ISWAP sama da 20 a tafkin Chadi


Gamayyar sojin haɗin gwiwa ta MNJTF sun yi nasarar kashe mayaƙan ISWAP da Boko Haram aƙalla su 22 a yayin wani farmaki da suka kai yankin na tafkin Chadi.


Laftanar Kanar Kamarudden Adegoke wanda shine babban jami'in yaɗa labaran rundunar haɗin gwiwa ta MNJTF shine ya bayyana nasarar da suka samu na kashe mayaƙan na ISWAP a wata sanarwa da ya fitar a ranar Asabar


Babban jami’in yada labaran rundunar hadakar a N’Djamena, Laftanar Kanar Kamaruddeen Adegoke ne ya bayyana haka a wata sanarwa da ya fitar a ranar Asabar. Inda yace mayaƙan sun haɗu da ajalinsu ne a Tumbun Rabo na yankin ƙaramar Hukumar Abadam a jihar Borno ranar 27 ga watan Afrilu.


Ya ƙara da cewa bayan yin gumurzu da suka yi da mayaƙan ne wanda suka samu taimakon rundunar sojin sama ta musamman wanda hakan yasa suka yi nasara akan mayaƙan. Bayan gumurzun mun tattara sakamako inda muka sami mayaƙan da suka rasa ransu su 20. Sannan kuma munyi nasarar ƙwace makaman su da bindigogi masu ƙirar AK-47 da motocin yaƙi, a cewar Adegoke.


A ƙarshen sanarwar ya ƙara da cewa za su ci gaba da yin farautar mayaƙan a duk inda suke domin yin maganin su. Yace ba za su yi ƙasa gwiwa ba har sai sun kawo ƙarshen aikin ƴan ta'ada.

Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post