Gwamnan Jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje ya bayyana cewa gaskiya da rikon amana ce ta sa ya zaɓi Mataimakinsa, Dr. Nasiru Yusuf Gawuna da tsohon Kwamishinan Ƙananan Hukumomi, Murtala Sule Garo a Matsayin waɗanda za su gaje shi. Gwamna Ganduje ya bayyana hakan ne yayin taron masu ruwa da tsaki na Jam’iyyar APC,wanda a ka gudanar a gidan Gwamnati a ranar Talata.
Ganduje ya ce Gawuna mutum ne da ya riƙe amana tun lokacin da a ka naɗa shi a matsayin Kwamishina yayin daga bisani aka naɗashi a Matsayin Mataimakin Gwamna. Ya ce yana da tabbacin idan Gawuna ya zama Gwamnan Kano, al’ummar jihar za su samu cigaba sosai, inda ya ƙara da cewa mataimakin nasa na da ƙwarewa ta fuskoki da dama.
Ya ƙara da cewa, Gawuna ya riƙe muƙaman da ya riƙe tun daga Shugaban Ƙaramar Hukuma Sannan yayi Kwamishina kuma ya zama mataimaki. Ganduje ya ƙara da cewa irin dalilan da suka sanya ya zaɓi Gawuna irin su ne yasa ya zaɓo Murtala Sule Garo a Matsayin wanda zai yi takarar Mataimakin Gwamna.
Bayan ya karɓi fom dinsa na takarar Sanatan Kano ta Arewa wanda ƴan Majalisun tarayyya suka saya masa. Gwamna Ganduje ya miƙa fom ɗin takarar gwamna ga Dr. Nasiru Yusuf Gawuna da Murtala Sule Garo Wanda Dattawan jam’iyyar APC na Jihar Kano suka saya musu