Majalisar Kano ta sauya sunan Jami'ar Wudil (KUST) zuwa Aliko Dangote University


Majalisar zartarwa ta  jihar Kano ta amince da sauya sunan Jami’ar Wudil (KUST) zuwa Aliko Dangote University of Science and Technology (ADUST) Wudil.


Majalisar ta amince da shawarar kwamitin sake sunan KUST da sunan Aliko Dangote. Majalisar zartaswar jihar Kano ta amince da sauya sunan Jami’ar Kimiyya da Fasaha ta Jihar Kano (KUST), Wudil. 


Kwamishinan yaɗa labarai na jihar, Malam Muhammad Garba, wanda ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a ranar Asabar, ya ce ci gaban ya biyo bayan shawarar da kwamitin da jami’ar ta kai ziyara. 


Ya bayyana cewa a yanzu ana kiran makarantar da suna Aliko Dangote University of Science and Technology (ADUST), Wudil. Malam Garba ya ci gaba da bayanin cewa an mika amincewar ga majalisar dokokin jihar domin nazarin dokokin da suka dace da suka kafa jami’ar domin yin gyara.

Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post