Ana gudanar da bukukuwan Sallah, da suka haɗa da hawan dawaki, a karon farko cikin shekaru 4 a birnin Katsina da ke arewacin Najeriya. Sakamakon matsalar tsaro dake addabar ƙasar yasa aka ɗauki tsawon lokaci batare da an gudanar da shagulgulan Sallah ba. Sai dai bana an samu sauyi inda aka gudanar da sallar idi a masallatai da dama tare da yin hawan Sallah.
Mutane da dama, ciki har da matasa, sun yi hawan Sallah ƙarama a Masarautar Katsina bayan an yi shekaru 4 ba a yi ba, dalilin matsalar tsaro da jihar ke fama da itan na hare-haren ƴan bindiga, da kuma iftila'in korona da ta shigo a shekarar 2019, wanda yasa aka rufe wajen ibadu tare da dakatar da dukkan wasu bukukuwa.
Daga ƙarshe a wancen lokacin an dakatar da hawan Sallah da wasu bukukuwa ne sakamakon rashin tsaro da ya addabi jihar da kuma ɓarkewar annobar korona, wanda ta shafi tattalin arzikin Duniya gabaki ɗaya.
Kawo yanzu dai mazauna birnin Katsina sai murna da annashuwa suke yi sakamakon dawo da gudanar da bukukuwan Sallah da aka saba yi tun a shekarun baya.