Kalli Hotunan shirin bikin auren jaruma Ummi Rahab da mawaƙi Lilin Baba


Da alamu dai shirye-shiryen auren mawaƙi Lilin Baba da Jaruma Ummi Rajab ya kankama. Wanda aka daɗe ana shirya shi.



Sai dai babu wata majiya da ta bayyana lokacin da za'a ɗaura auren waɗannan masoya, amma dai alamu suna nuna cewa za'a yi bikin ne a kusa.



Ganin yadda aka fara ganin hotunan da masoya suke yi kafin a ɗaura aure wanda a turance ake kira da free-weding-pictures. Inda a ranar Laraba ake ganin hotunan masoyan yana yawo a kafafen sada zumunta na zamani.



Munyi ƙoƙarin tuntuɓar masoyan domin sanin haƙiƙanin lokacin auren na su sai dai ba mu samu damar yin magana dasu ba ko wasu makusantan su ba har lokacin haɗa wannan rahoto.

Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post