Tsohon Gwamnan Jihar Abia, Orji Uzor Kalu, ya ja hankalin jam’iyyar APC mai mulki a kan guguwar sauya sheƙa da a ke yi zuwa jam’iyyar NNPP. Kalu, wanda shi ne Bulaliyar Majalisar Dattawa, ya bayyana hakan ne a wata sanarwa da ya wallafa a sahihin shafin sa na Facebook cewa ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar NNPP, Rabiu Kwankwaso, zai samu damar lashe zaɓen shugaban ƙasa idan har guguwar sauya sheƙar nan zuwa jam'iyar ta sa ta ci gaba.
“Bai kamata manyan jam’iyyar mu ta APC su yi watsi da sauyin sheƙar sa ake ta yi a kwanakin nan zuwa sabuwar jam’iyyar NNPP ba, musamman a shiyyar Arewa-maso-Yamma. “Ina amfani da wannan dama wajen sake nanata matsaya ta ta farko cewa takarar shugaban ƙasa ta tafi yankin Arewa maso Gabas idan har ba za a iya ba yankin Kudu maso Gabas ba.
“Mafi rinjaye na waɗanda su ke ganin an yi musu rashin adalci za su iya mara wa Engr. Rabiu Kwankwaso baya har ya lashe zaɓen shugaban kasa a 2023 idan jam'iyyar mu, APC da PDP suka tsayar da ƴan takararsu daga kowane shiyyar baya ga Kudu maso Gabas ko Arewa maso Gabas. "Lokaci ya yi da za mu haɗa kai mu mara wa yankin da bai samar da shugaban ƙasar ba baya tun bayan taron karba-karba da aka fara a 1999," in ji Mista Kalu.
Jam'iyar NPP dai sabuwar jam'iyya ce da ake tunanin zata taɓuka wani abu a zaɓen da za'a gudanar a 2023. Kawo yanzu jam'iyyar tana ta samun baƙi daga manyan jam'iyyun APC da PDP wanda daga ciki akwai sanata Rabi'u Musa Kwankwaso da sauran wasu manyan ƴan siyasa.