Breaking News
DSS ta kama ƴan boko haram da kayan haɗa bama-bamai zasu shiga Jihar Kano
Saturday, May 21, 2022
0
Rundunar jam'ian farin kaya ta DSS reshen jihar kano, tayi nasarar kame wasu mayaƙa da ake zaton ƴan Boko Haram ne su 2 cikin wata mota, tare da kayayyakin haɗa bama-bamai a hanyarsu ta dab da shiga garin kano."
DSS ɗin ta kama mayaƙan ne da muggan makamai da suka haɗa da bindigu ƙirar AK47 biyo bayan wasu kayayyaki na haɗa bama-bamai kamar yadda jam'ain suka bada sanarwan hakan, tare da bayyana hakan acikin hotuna.
Idan baku manta ba a makon da ya gabata ne aka samu labarin fashewar wani abu da ake tunanin cewa bam ne a unguwar Sabon Gari dake cikin birnin Kano, sai dai daga bisani an tabbatar da cewa ba bam ne ba tukunyar girki ce ta gas.
Previous article
Next article
Leave Comments
Post a Comment