Ba Zanyi Ritaya Daga Siyasa Ba Har Sai Na Zama Shugaban Ƙasa - Bola Tinubu


Mai neman takarar Shugaban Ƙasa ƙarƙashin jam’iyyar APC, Sanata Bola Ahmed Tinubu ya ce ba zai daina siyasa ba har sai ya cika burinsa na son zama Shugaban ƙasar Najeriya.


Ɗan siyasar ya yi wannan furuci ne a Makurɗi babban birnin Jihar Binuwai, yayin ziyarar da ya kai Jihar a ranar Talata don neman goyon bayan daliget, gabanin zaɓen fidda gwani mai zuwa na APC.


Tinubu ya yi kira ga matasan Jihar da su tabbatar sun mallaki katin zaɓensu, tare da ba su tabbacin shi da mutanensa suna tare da matasan don haɗa hannu wajen bunƙasa haɗin kai da ci gaban Najeriya.


“Duk da dai shekarunmu sun ja, za mu bar siyasa nan kusa idan kun so, amma ba zan daina siyasa ba sai bayan na zama Shugaban Najeriya. Ya ƙara da cewa, muddin aka zaɓe shi a matsayin Shugaban Ƙasa, gwamnatinsa za ta maido wa talakawan Najeriya ƙarsashin da suka rasa.


Hakazalika ya ce, idan APC ta tsayar da shi a matsayin ɗan takararta, babu wata ja-in-ja da za a samu tsakaninsu da ɗan takarar jam’iyyar hamayya ta PDP. Daga nan, ya jaddada cewa idan ya samu mulkin ƙasa zai ɗora Najeriya a kan salon mulkin da ya yi amfani da shi sa’ilin da yake Gwamnan Legas don samun daidaito.


Ko a makon da ya gabata anjiyo Ahmad Tinubu yana bayyana cewa shi kaɗai ne ɗan takarar shugaban ƙasa a jam'iyyar APC. Wanda wasu ke bayyana cewa rikicin tsufa ne ke damun sa. Sai dai shi ya sha bayyana cewa yana cikin ƙoshin lafiya babu abinda ke damun sa.

Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post