Ƴan bindiga sun yi garkuwa da mutane kusan 20 ciki har da mai gari a jihar Kaduna


Ƴan bindiga sun kashe aƙalla mutum ɗaya tare da sace mutum 16 ciki har da mai gari a unguwar Kurmin Sata dake Ƙaramar Hukumar Chikun a Jihar Kaduna.


Jaridar Daily Trust ta rawaito cewa, lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 12:16 na daren ranar Asabar, yayin da maharan suka yi wa garin ƙawanya, suka dinga harbi kan mai uwa da wabi.


Wata majiya daga jami’an tsaron haɗin guiwa ta JTF ta ce “Mai gari da sauran yara da mata na daga cikin waɗanda maharan suka sace; wanda ya rasu kuwa harsashi ne ya same shi lokacin yana cikin gida yayin da suke harbi,” cewar majiyar.


Majiyar da ta buƙaci a sakaya sunanta ta bayyana cewa da farko mutum 20 ƴan bindigar suka sace, kafin daga bisani wasu daga cikin mutanen suka tsere, yanzu haka mutum 16 ke hannunsu. Sai dai jin ta bakin kakakin ’yan sandan jihar Kaduna, ASP Jalige Mohammed, ta ci tura sakamakon rashin amsa wayarsa.


Hare-haren ƴan bindiga a wasu sassan jihar Kaduna yai ƙamari, domin a wannan lokutan zai wuya kaga anyi mako guda batare da kai hare-hare ba. Sai dai mahukunta na iƙirarin cewa suna ɗaukar matakai wajen ganin sun shawo kan wannan matsalar ta tsaro a jihar ta Kaduna.

Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post