Ƴan Bindiga Sun Hallaka sama da mutane 350 a jihar Kaduna a watanni 3


Samuel Aruwan, Kwamishinan Tsaro da Harkokin cikin gida na Jihar Kaduna,  ya ce an kashe mutane a ƙalla 360 ​​tsakanin watan Janairu zuwa watan Maris 2022 ta hanyar fashin jeji da kuma rikicin ƙabilanci.


Kwamishinan ya bayyana haka ne a lokacin da yake gabatar da rahoton zangon shekara na farko kan tsaro na shekarar 2022 ga gwamnan jihar, Nasir El-Rufai, a jiya Alhamis a Kaduna.


Ya ce an yi garkuwa da mutane 1,389 a iya lokacin da ake binciken a yankin Kaduna ta tsakiya. An yi garkuwa da mutane 169 daga Birnin Gwari, Giwa 158, Igabi 263, Chikun 287 da kuma Ƙaramar Hukumar Kajuru da a ka yi garkuwa da mutane 203, cewar Aruwan.


A cewarsa, aƙalla mutane 249 ne aka yi garkuwa da su a sakamakon hare-haren ƴan bindiga da wasu muggan hare-hare da aka kai a yankin Kudancin Kaduna a dai wannan lokacin da aka yi wannan binciken.


Ya bayyana cewa mutane 258 ne su ka samu raunuka a faɗin jihar sakamakon rikicin ƴan fashi, rikicin ƙabilanci, yana mai cewa 38 daga cikin waɗannan alƙaluma mata ne kuma 11 ƴan kasa da shekaru 18 ne.


Aruwan ya ce an sace dabbobi 3,251 a tsawon lokacin, inda 3,137 aka sace daga Kaduna ta Tsakiya, wanda ya kai kashi 97 cikin 100 na adadin. 

Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post