Shahararren mawaƙin wakokin siyasa a Kannywood, Dauda Adamu Abdullahi Kahutu Rarara ya saka murna a fuskar wasu ƴan Kannywood fiye da mutum 50 da kyautar tsabar kuɗi har ₦50,000 ga kowannensu.
Rabi'u Garba wanda shine hadimin mawaƙin kan kafafen watsa labarai, shine ya bayyana hakan, inda ya ce tallafin na ciki ire-iren ayyukan ƙungiyar 13×13, wadda Rarara ke jagoranta. A cikin sanarwa da ya sanya wa hannu, ya ce an bai wa jarumai iyaye mata 13 da jarumai iyaye maza 15 kyautar 50,000 kowannensu.
Sannan ya ce Rarara ya bai wa jarumai mata 10 kowanensu kyautar 50,000, yayin da kuma mawaƙa mata masu aure suka samu kyautar 30,000 kowannensu. Tuni waɗanda suka ci gajiyar tallafin suka shiga bayyana godiyarsu ga mawaƙin a shafukansu na sada zumunta.
Sabuwar tafiyar 13×13 wadda Rarara ke jagoranta ta ƙunshi jarumai, mawaƙa, furodusoshi da daraktoci daga masana’antar shirya fina-finan Kannywood a matsayin ƴaƴan ƙungiyar.
Idan ba a manta ba a baya-bayan nan mambobin 13×13 suka dawo daga birnin Dubai na ƙasar Hadaddiyar Daular Larabawa (UAE) inda suka je yawon shaƙatawa da ƙungiyar ta ɗauki nauyi.
Mawaƙin dai ba wannan ne karo na farko da ya saba raba kuɗi ga ƴan Ƙannywood, ko a shekarar da ta gabata sai da ya raba kuɗaɗe ga jarumai a masana'antar. Baya ga kyautar kuɗaɗe kuma, Rarara ya sha yin kyautar motoci ga mutane daban-daban a masana'antar Ƙannywood.