Yan bindiga sun sace jarirai a Zaria


Wasu Yan bindiga a Jihar Kaduna dake Najeriya sun kai hari a wani asibiti da ake kula da masu fama da cutar tarin fuka da kuturta dake Zaria inda suka kwashi jarirai.


AL’AJABI: ‘Yar Aiki Ta Tsere Da Jaririn Gidan Da Take Aikatau A Kaduna.

KARANTA: Duk Gwamnan dake son Jiharsa ta Zauna Lafiya ya Koma APC, Gwamna Matawalle

KARANTA: Duniya Na Fuskantar Tsadar Abinci Mafi Muni A Cikin Shekara 10


Jaridar Daily Trust da ake wallafawa a Najeriya tace Yan bindigar sun kwashi ma’aikatan asibitin guda 5 cikin su harda mata masu taimakawa likita.


Rahotanni sun ce Yan bindigar da suka kutsa kai cikin asibitin da yawa sun yi ta musayar wuta da jami’an Yan Sandan dake wata tashar Yan Sanda kusa da wurin.


Wani shaidar gani da ido yace anyi musayar wuta sosai tsakanin maharan da jami’an Yan Sandan kafin su kwashi mutanen cikin su harda babban jami’in tsaron asibitin.



Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post