An kama wata mata mai suna Dayane Cristina Rodrigues Machado akan zargin ta na kashe mai gidan ta tare da yanke mazakutarsa ta soye.
KARANTA: Mulkin Soja Ake Yi A Kaduna Ba Dimokuradiyya Ba, Isa Ashiru
KARANTA: Yan bindiga sun sace jarirai a Zaria
KARANTA: Duniya Na Fuskantar Tsadar Abinci Mafi Muni A Cikin Shekara 10
Jaridar Aminiya ta rawaito cewa matar mai shekara 33, an kama ta ne a garin Sao Goncalo na yankin kasar Brazil a ranar 7 ga Yunin bana bayan gano gawar mijinta mai suna Andre.
An kira ’yan sanda zuwa gidan ma’auratan a Unguwar Santa Catarina kuma sun iske gawar tsirara an yanke wasu bangarori na jikinsa.
’Yan sanda sun samu wuka a wurin da ake zargin ta aikata kisan ce, inda alamu suka nuna cewa, ita ce ta kashe mijin ta kuma ta yanke wasu sassan jikinsa.
An kama Machado a wurin kuma tun daga lokacin aka zarge ta da kisan kai.
A cewar wani gidan kafar labarai ta UOL, sun bayyana cewa ma’auratan sun fita zuwa gidan cin abinci a daren da aka aikata kisan, sai rikici ya barke a tsakaninsu.