Sheikh Abdul-Jabbar Ya Shafe Daren Farko A Gidan Yari



Sanannen malamin addini da aka fi sani da Abduljabbar Nasir Kabara ya shafe daren sa na farko a hannun yan sanda




An gurfanar da malamin ne ranar Juma'a, kan zargin sa ga batanci ga Annabi Muhammad SAW da sahabban sa da kuma tunzura jama'a, wanda malamin ya sha musanta wannan zargin.





Wata sanarwa da kwamishinan yaɗa labarai na jihar Kano Muhammad Garba ya fitar, yace an gurfanar da Malam Abdul-Jabbar ne, "wanda ya yi ƙaurin suna wajen yin wa'azi wanda kan haifar da muhawara, saboda zargin furta kalaman da ka iya haifar da tunzuri, da kuma bata sunan Annabin Allah''.



Kotu dai ta dage zamanta har zuwa ranar 28 ga wannan watan na Yuli da muke ciki domin cigaba da sauraren Shari'ar.



Kuma an bayyana cewa malamin zaici gaba da zama karkashin kulawar hukumar yan sanda har zuwa Litinin wanda kuma daga nan ne za'a Kaishi gidan yari domin yaci gaba da zama a can har zuwa ranar 28 ga watan Yuli. 
Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post