Alhaji Isah Muhammad Ashiru tsohon dan Majalisar Jihar Kaduna ne, kuma ya taba zama dan Majalisar Wakilai, kafin ya yi takarar neman zama Gwamna Jihar Kaduna a zaben shekarar 2019 a Jam’iyar PDP.
A zantawarsa da Aminiya ya zargi gwamnatin APC a jihar kan yadda take tafiyar da mulkinta inda ya ce mulkin soja ake yi a jihar ba dimokuradiyya ba:
Me kake ciki tun bayan faduwarka zaben 2019?
Bayan zaben 2019 na yi tunanin komawa gona da harkar kasuwanci na saye da sayarwa. Tun zuwan wannan gwamnati, sai na ga lokaci ne da zan zauna da iyalaina in huta na wani lokaci.
Amma daga wancan lokaci zuwa yanzu jam’iyarmu ta yi nasarar gudanar da zaben
shugabanninta da za su tafiyar da harkokinta.
Me ya sa kake ji ya jawo ka fadi a shekarar 2015 da 2019 da ka fito takarar Gwamna?