Yadda Ƴan bindiga suka rika rusa bangon ɗakunan mutane suka sace mutum goma 13 a Kaduna
Mazauna unguwar Gimbiya dake Sabon Tasha, garin Kaduna sun tashi da safiyar Alhamis cikin tashin hankali bayan wasu ƴan bindiga sun afka musu cikin daren Laraba.
KARANTA: Gwamnatin Kano Ta Fitar Da Ranar Yin Muqabala Da Sheikh Abdul-Jabbar
KARANTA: Shin Kun San Cewa Zaku Iya Amfani Da Bawon Ayaba Ku Wanke Hakoran Ku Suyi Haske?
KARANTA: El-Rufai Ya Bada Umurnin Rufe Makarantu 13 a Kaduna Litinin,
Jaridar Libert ta rawaito cewa, Maharan sun afka wa wannan unguwa ne cikin dare suna harbe-harbe ta ko ina don tsorata mutane sannan suka dunguma zuwa gidajen mutane suna sace su.
” Wannan salo na yin garkuwa da mutane ya bamu tsoron gaske, domin don ka garkame gidan ka da kwaɗo ko ka saka waya a saman katangar duk ba wani abin damuwa ba ne gare su. Katanga suke fasawa ko kuma ma bangon ɗakin ka ta waje sai su rusa shi su shigo maka daki.