Mutane da-dama suna tunanin cewa Dalar Amurka ko Euro ko kuma kudin Birtaniya ne ya fi kowane daraja a fadin Duniya, amma ba haka abin yake ba.
Duk da cewa Dalar Amurka da irins Pound Sterling su na da daraja, Highest Currency ta ce akwai kudin da suka sha gabansu, daga ciki akwai Dinarin Kuwait.
Dinaran kasashen Kuwait da Bahrai sun ninka Dalar Amurka sau 3.29 da 2.65. Haka zalika akwai kudin Omani riyal da shi ma ya sha gaban Dalar ta Amurka.
Jordanian Dinar da Gibraltar Pound su ne suka cika rukunin sahun biyar na farko a wannan jeri.
A halin yanzu, Highest Currency ya nuna Pound Sterling, Euro, da Dalar Amurka sune na shida, takwas da na tara a cikin kasashen da suka fi daraja a Duniya.
1. Kuwaiti Dinar
2. Bahrain Dinar
3. Omani Riyal
4. Jordanian Dinar
5. Gibraltar Pound
6. Pound Sterling
7. Cayman Island Dollar
8. Euro
9. US Dollar
10. Swiss Franc
Swiss Franc, da Dalolin kasashen Brunei, Kanada, New Zealand, Australia da Fiji sun cira tuta. Kudin Libyan Dinar shi ne kudin da ya fi kowane daraja a Afrika.
11. Brunei Dollar
12. Canadian Dollar
13. Australian Dollar
14. Libyan Dinar
15. Singapore Dollar
16. New Zealand Dollar
17. Fijian Dollar
18. Brazilian Real
19. Israel New Shekel
20. Turkish Lira
A tsakiyar makon nan ne aka ji cewa darajar Naira ta kara sukurkucewa bayan CBN ta daina ba ‘yan canji Dalar Amurka saboda zargin suna yin ta’adi. Daga hana ‘yan kasuwa kudin kasashen waje, Dalar Amurka ta fara zabura a kasuwar canji. Rahotanni sun bayyana cewa Dala $1 ta koma Naira 505.