Gwamnonin Kudancin Najeriya sun Ce Dole a ci gaba da karba-karba


KARANTA: El-Rufai Ya Bada Umurnin Rufe Makarantu 13 a Kaduna Litinin,

KARANTA: Wata Mata Ta Yanke Azzakarin Mijinta Ta Soye Shi

KARANTA: Yan bindiga sun sace jarirai a Zaria


Gwamnonin Jihohin dake kudancin Najeriya sun bukaci mayar da mulkin kasar zuwa yankin su bayan kammala wa’adin mulkin shugaban kasa Muhammadu Buhari a shekarar 2023 domin ci gaba da karba karba tsakanin arewa da kudu.


Wannan matsayi ya biyo bayan taron da Gwamnonin suka gudanar yau a Lagos wanda ya jaddada matsayin su kan batutuwa da dama da suka shafi halin da Najeriya ke ciki da suka hada tsaro da kuma tattalin arzikin kasa.


Sanarwar bayan taron da Gwamnan Ondo Rotimi Akeredolu ya rabawa manema labarai tace sun yi nazarin halin tsaron da Najeriya ke ciki inda suka jinjinawa jami’an tsaro saboda rawar da suke takawa wajen kare lafiya da dukiyoyin jama’a, yayin da suka mika sakon ta’aziya ga jami’an da suka rasa rayukan su.

Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post