Zainab Booth, tsohuwar fitacciyar jarumar Kannywood kuma uwa ga Maryam Booth, ta mutu.
KARANTA: Dan wasan Najeriya Shehu Abdullahi ya auri 'yar film Naja'atu 'yar Baba
KARANTA: Illolin yin jima'i ta dubura ga lafiyar jiki
KARANTA: Illolin dake faruwa da Budurwar da ta bari Saurayin ta yai zina da ita
Abokin aikinta, Ali Nuhu ne ya sanar da hakan ta shafinsa na sada zumunta na instagram wanda ya tabbatar da hakan, ta rasu ne a ranar Alhamis. A cewar Ali Nuhu.
Ya bayyana cewa za a yi jana’izar marigayiyar ’yar fim a gidanta, da ke kusa da Asibitin Premier, a titin Kotu( court road), Kano, da karfe 8 na safiyar yau, Juma’a.
Ta rasu tana da shekaru 61 a duniya.
A kwanakin baya ne dai marigayiyar ta yi fama da rashin lafiya lamarin da ya kai har an yi mata aiki a kwakwalwa, kamar yadda 'yarta Maryam Booth ta dinga wallafa hotunan a shafukan sada zumunta.
Marigayiyar ta kasance daya daga cikin taurarin Kannywood da 'ya'yanta uku suka kasance su ma taurari.