Falalar Goman Farko Na Watan Dhul-Hijjah, yi kokari kayi ayyukan alheri domin Rabauta daga Rahamar Allah.
KARANTA: Siffofin Da Suke Hana A Auri Mace
KARANTA: Mahaifiyata ta Rasu Ana binta Azumi, Shin Zamu iya rama mata?
KARANTA: Illolin kallon fina-finan batsa
1. Ya zo a cikin "Sahihul Buhari" Hadisin Abdullahi Dan Umar RA, Cewa Annabi S.A.W. ya ce, "Babu wasu Kwanaki da aiki nagari ya fi soyu wa zuwa ga Allah fiye da wadannan Kwanaki Goman (yana nufin goman Dhul - Hijjah) Sai suka ce: _koda Jihadi Fi SabililLah?_ Ya ce: Koda _(_Jihadi Fi SabililLah_ )_ Sai dai Mutumin da ya fita da ransa da dukiyarsa bai dawo da komai ba."
2. Lalle kwanaki ne masu mutukar daraja, Saboda darajarsu ne ma Allah SWT da Kansa Yai rantsuwa dasu a cikin a farkon "Suratul Fajri" saboda ya nuna Mana girmansu da falalarsu.
3. -An tambayi Shaikhul Islam cewa, da goman farko na "Dhul Hijjah" da goman karshe na "Ramadan" wadanne suka fi falala? Sai yace: Idan ta fuskar yini ne, to goman farkon Dhul Hijjah sun fi. Idan kuma ta fuskar darare ne, to goman karshe na Ramadan sun fi. "Duba Fatawal Kubra, Juz'i na 2 Shafi na 477."
4. Ayyukan alkhairi sun hadar da: yawan ambaton Allah. Ya zo cikin "Musnad na Ahmad" daga Dan Umar R.A. cewa: Annabi SAW ya ce: "babu wasu kwanaki da suka fi girma a wajen Allah ko suka fi soyu wa a wajen sa daga aiki a cikin su fiye da wadannan kwanakin goma na Dhul Hijjah. Don haka ku yawaita "Hailala da Kabbara da Hamdala" a cikinsu".
5. Daga cikin ayyukan alkhairi akwai Karatu Alkur'ani da Tudabburi a cikinsa. Don haka 'Yan uwa masu daraja, mu dage da Karatun Alkur'ani a cikinsu.
6. Sauran ayyukan alkhairi sun kunshi Sada Zumanta da Taimakon 'Yan uwa. Ya zo a cikin hadisi cewa: Duk Wadda yake so a Yalwata Masa cikin Arzikinsa kuma a Tsawaita Masa cikin Shekarunsa to ya Sada Zumuntar sa."
7. Haka kuma, Azumi yana daga cikin Ayyuka Nagari masu Falala da mutum zai ribata a wadannan "Kwanuka Guda Tara," Idan bai azumce su duka ba to kada ya Bari Azumin Ranar Arfa wato ranar 9 ga wata ya wuce shi. Domin Yana Kankare Zunubin Shekara - 2 Kamar yadda yazo a Sahih Muslim, Hadisin Abiy Qatadah.
8. Sadaka: ta Wajibi (zakka) ko ta Nafila suna daga cikin ayyuka nagari da zaka ribata a wadannan kwanukan. Ya zo a cikin hadisi cewa: "ka ji Tsoron Wuta Ko da ta Tsagin Dibino ne, idan baka samu ba, to Ko da tahijriyy Kalma ce"
9. Har ila yau ayyukan alkhairi sun kunshi: duk abinda Allah Ya ke so kuma ya yarda da shi. To ka yi iya yinka ka ga ka yawaita shi a wadannan kwanakin;
10. Ya Dan uwa Wanda ka yi sakaci a Ramadan, ga dama ta samu, yau ake gobe sai labari. Don haka kada ka Bari wadannan Gwala-gwalen kwanukan su wuce ka ba tare da ka Habbaka Asusunka na lahira ba.
Allah Ya sa mu dace Amin, Abu Awanatal Kanawiy