Alkaluman da hukumar ta fitar ya nuna cewa, farashin kayan abincin a baya-bayan na tashi cikin sauri a kusan dukkan sassan Duniya, cikin wani yanayi da ba a taba gani ba a shekaru 10 da suka gabata.
KARANTA: Hanyoyi 7 Da Zaki Gane Namiji Mai Nagarta
KARANTA: Yan Bindiga Sun Sace Mata 13 A Jihar Kaduna
KARANTA: Siffofin Mutane Masu Jin Tsoron Allah
A cewar hukumar ta FAO annobar covid-19 ta taimaka matuka wajen kara karanci da kuma tsadar abinci a sassan Duniya da akalla kashi 40 wanda ke matsayin tashi mafi tsanani da aka gani tun bayan shekarar 2011.
Shugaban sashen tattalin arziki na FAO Arif Husain ya ce farashin masara ya karu da kashi 88 yayinda waken suya ya karu da kashi 73 kana kayan abinci nau’ikan hatsi da mayukan girki ya karu da kashi 38 kana sukari da kashi 34 sai nama da kashi 10, alkaluman da jami’in ke cewa barazana ce ga tattalin arzikin Duniya.