Gwamnan jihar zamfara Bello Matawalle ya jaddada dalilin sa na barin jam’iyyar PDP zuwa jam’iyyar APC.
KARANTA: Duniya Na Fuskantar Tsadar Abinci Mafi Muni A Cikin Shekara 10
KARANTA: Yan Bindiga Sun Sace Mata 13 A Jihar Kaduna
KARANTA: Hanyoyi 7 Da Zaki Gane Namiji Mai Nagarta
Gwamnan a Wata hira da gidan talabijin na TOS yayi dashi ya bayyana cewa yayi kaura daga PDP din ne zuwa APC saboda yawaitar kashe – kashen al'umma da ake samu a jahar sa.
Ya yi kira ga sauran gwamnonin da Jahar su ke fama da matsalar rashin tsaro da su gaggauta komawa jam’iyyar APC mai rinjaye domin samun wanzuwar zaman lafiya a jahohin su.
Ya ce “Na yanke shawarar chanja jam’iyya ne saboda na kawo zaman lafiya a jaha ta, yanzu da duk muka kasance ‘yan jam’iyya daya zan samu cikakken goyan bayan gwamnatin tarayya domin kawo karshen rashin zaman lafiya a Jahar zamfara.