'Yan Bindiga Sun Sace Mata 13 A Jihar Kaduna



Yan bindiga a Najeriya sun sace mata 13 tsakanin garuruwan Manini da Udawa akan hanyar Kaduna zuwa Birnin Gwari, dake fama da matsalar tsaro.


KARANTA: Hanyoyi 7 Da Zaki Gane Namiji Mai Nagarta

KARANTA: Nnamdi Kanu ya bayyana wa kotu dalilan da yasa ya gudu

KARANTA: Illolin dake faruwa da Budurwar da ta bari Saurayin ta yai zina da ita


Jaridar Daily Trust ta rawaito cewar Yan bindigar sun tare motoci guda 3 dake dauke da matan ne da misalin karfe 12 na ranar Alhamis inda suka tafi da su.


Jaridar tace daga cikin matan da aka sace akwai mata masu shayarwa da wata kuma dake tare da ‘yayan ta mata guda 5 sai kuma wani karamin yaro mai shekaru 7.


Wani shugaban al’umma Mohammed Umar ya shaidawa jaridar cewar daukacin matan 13 sun fito ne daga Udawa akan hanyar su ta zuwa biki a Birnin Gwari.


Umar yace wasu daga cikin matan sun fito ne daga gida guda kamar Zainab Abu Jibril dake tafe da ‘yayan ta mata guda 5 wadanda ke cikin tawagar.


Jami’in yace zuwan jami’an soji ya sa Yan bindigar suka bar wurin, abinda ya hana su kwashe mutane da yawa daga inda suka tare hanya suna kwashe wadanda basu da labarin zaman su a wurin.

Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post