An Yankewa Masu Satar Mutane Hukuncin Daurin Rai Da Rai A Sokoto
Yadda aka yanke wa wasu masu satar mutane hukunci na É—aurin rai da rai a jihar Sokoto.
KARANTA: Gwamnonin Kudancin Najeriya sun Ce Dole a ci gaba da karba-karba
KARANTA: Yan bindiga sun sace jarirai a Zaria
KARANTA: El-Rufai Ya Bada Umurnin Rufe Makarantu 13 a Kaduna Litinin,
Ƴan uwa da masu rajin kare haƙƙin ɗan adam sun bayyana ra'ayoyinsu a kan hukuncin ɗaurin rai-da-rai da Babbar Kotun Tarayya ta yanke wa wasu masu garkuwa da mutane huɗu a jihar Sokoto da ke arewa maso yammacin Najeriya.
Kotun dai ta yanke musu wannan hukunci ne bayan ta same su da laifin garkuwa da wani fitaccen É—an kasuwa a shekarar 2013, lamarin da ya yi sanadin mutuwarsa saboda jigata da É—imautar da yayi.
Ba kasafai ake jin kotuna na yanke wa masu satar mutane hukunci irin wannan hukunci ba, musamman a yankin arewacin ƙasar, inda hare-haren ƴan fashin ke ƙara ta'azzara.
Duk da tsawon shekarun da aka kwashe bayan sace wa tare da yin garkuwa da marigayi Alhaji Abubakar Dankure, makusantan É—an kasuwar sun ce É—aurin rai-da-rai da kotu ta yanke wa masu garkuwar ya rage musu zafi da raÉ—aÉ—in aika-aikar da aka tafka musu.
Leave Comments
Post a Comment