AL’AJABI: ‘Yar Aiki Ta Tsere Da Jaririn Gidan Da Take Aikatau A Kaduna.


A Unguwar Tudun Wada da ke Jihar Kaduna ce wata ‘yar aikin gida mai shekara 16 a duniya tayi awon gaba da jariri dan wata 10 a gidan da take aiki.


KARANTA: Hanyoyi 7 Da Zaki Gane Namiji Mai Nagarta

KARANTA: Duk Gwamnan dake son Jiharsa ta Zauna Lafiya ya Koma APC, Gwamna Matawalle

KARANTA: Duniya Na Fuskantar Tsadar Abinci Mafi Muni A Cikin Shekara 10


Bayanai sun ce uwar jaririn mai suna Fauziyya Aminu Tukur, ta bar jaririn ne a wajen ‘yar aikin yayin da ta tafi makaranta zana jarrabawa, amma bayan daworta sai ta riski gidan babu kowa.


Mahaifiyar jaririn ta bayyanawa manema labarai cewar, tana barin ‘yar aikin tare da jaririn a gidan makota, a duk lokacin da za ta je makaranta.


“Bayan na dawo daga makaranta sai na zarce zuwa gidan makociyata, sai ta shaida min bata zo ba.


“Ko da na koma gida ina tunanin ko bacci ya dauketa, na dinga bugun kofa amma shiru, sai na kira mijina yazo da makullin wajensa muna bude gida muka tarar bata ciki, mun duba ko ina bata nan,” a cewarta.

Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post