Muhammad Shamsudden yaro ne mai karancin shekaru wanda ba kasafai aka fiya samun yara Kamar sa masu karancin shekaru da irin wannan baiwar ba.
KARANTA: Muhimmanci gwajin kwayar halitta kafin ayi aure
KARANTA: Yar Aiki Ta Tsere Da Jaririn Gidan Da Take Aikatau A Kaduna.
KARANTA: Duniya Na Fuskantar Tsadar Abinci Mafi Muni A Cikin Shekara 10
A hirar sa da gidan Radio Bbc Hausa Malamin mai shekaru takwas ya bayyana cewa an kaishi makaranta ne tun bayan an yaye shi.
Malamin kuma ya ce duk da cewa ya yi makaranta amma ya samu karatu ne ta hanyar baiwa daga Allah da kuma tallafin mahaifinsa.
Yanzu dai baya ga tafsirin al-qur'ani, Shamsuddeen ya sauke littafai kamar Kawa'idi, Ahlari da Risala da Ishamwiy da Mukhtasar da dai sauran litattafai.
Malamin ya kan hau kujerar mahaifinsa ta bai wa manya karatu ko kuma tafsirin al-qur'ani mai girma a watan Ramadan.
Sai dai duk da cewa Muhammad Shamsuddeen ya zama shehin malami a fagen addinin Musulunci, yace burinsa shi ne kasancewa lauya a nan gaba Ko likita.