Abin Mamaki: Shin Kun San Cewa Zaku Iya Amfani Da Bawon Ayaba Ku Wanke Hakoran Ku Suyi Haske?


Abin Mamaki: Shin Kun San Cewa Zaku Iya Amfani Da Bawon Ayaba Ku Wanke Hakoran Ku Suyi Haske?


Masana kiwon lafiyar hakori suna bada shawarar cewa mutum ya ringa amfani da bawon ayaba yana gogawa a hakoran sa Kamar na tsawon minti 2 a rana. Sunce yin amfani da bawon ayaba wajen gurzawa a hakora yana inganta lafiyar hakori da cire dukkan wani datti dake makale a jikin hakora.


KARANTA: Yadda Zaki Kula Da Lafiyar Nonon ki Da Kanki Batare Da Kinje Asibiti Ba

KARANTA: Idan kasan baka iya yin mintuna 8 kana jima'i ka gaggauta yin wannan hadin

KARANTA:  Sahihin Maganin Zazzabin Maleria, Cizon Sauro


Haka ne, Zaku iya cewa wannan abu ne mara kyau, amma a zahiri za ku iya yin amfani da bawon ayaba don goge haƙoranku. Duba da irin sinadaran dake jikin bawon wanda ke sanya shi mahimmanci a haƙoran. 


Idan ka tashi Wanke Hakoran ka, sami ayaba cikakkiya(nunanniya) wacce batayi ja ba kuma ba rubabiya ba.

Ga makatakan da Zaku bi domin goge hakoran naku.



(1) Samu ayabar ka mai kyau ka bare 

Ku Sami ayaba wacce take mai kyau ba wadda ta lalace ba. Kuma anaso a Samu mai girma wacce ta nuna (wacce take da sinadarai mai karfi a jikinta)


(2) Shafa bawon a jikin hakoran ka

Ku goga bawon na tsawon minti goma a hakoran ku na sama da na kasa ku goge Ko Ina na hakoran, ku tabbatar wannan sinadarin na bawon ayaba ya taba kowa Ina na cikin hakorin.



(3) Goge hakoran da Burushi

Da zarar mintuna goma sun cika da shafa bawon ayabar, ɗauki burushi busashe ka goge hakoran naka dashi.


4. Kayi haka kowace rana

Abu ne mai wuya kaga sauyi a lokaci daya, amma idan zaka juri yin hakan na tsawon sati biyu, zakayi mamaki yadda hakoran ka zasu canja, zasu yi fari suyi hakse kuma suyi kwari. 

Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post