A Najeriya hukumomi sun bayyana cewa an kama Nnamdi Kanu, Shugaban kungiyar IPOB wanda ke neman warewa daga kasar.
KARANTA: Illolin yin jima'i ta dubura ga lafiyar jiki
KARANTA: Illolin dake faruwa da Budurwar da ta bari Saurayin ta yai zina da ita
KARANTA: Siffofin Da Suke Hana A Auri Mace
Shafin jaridar Bbc Hausa ya rawaito cewa Abubakar Malami wanda shine Ministan Shari'an kasar ya tabbatar da kama Mr Kanu a taron da yai ga manema labarai a Abuja ranar Talata.
Ministan ya kara da cewa an kama shugaban IPOB ne ranar Lahadi kuma za a gurfanar da shi a gaban kuliya kan zarge-zargen da ake yi masa na neman warewa daga Najeriya.
Kanu yana fuskantar zarge-zargen da suka shafi cin amanar kasa lamarin da ya sa aka gurfanar da shi a gaban wata babbar kotun tarayya da ke Abuja bisa yunkurin da yake yi wajen ganin an kafa kasar Biafra ta hanyar IPOB.
A watan Afrilu na shekarar 2017 aka bayar da belinsa bisa dalilai na rashin lafiya sai dai ya gudu daga kasar.
Wanda kuma daga bisani ne jami'an tsaron Najeriya suka furta kungiyar IPOB a matsayin kungiyar 'yan ta'adda