Yanzu-Yanzu JAMB ta saki sakamakon jarabawar UTME ta wannan shekarar


Hukumar shirya jarabawar shiga makarantun gaba da sakandire JAMB ta saki sakamakon jarabawar UTME ta wannan shekarar.


KARANTA: Yan sanda sun tabbatar da sace mutane 12 a jihar Kaduna

KARANTA: Yan Bindiga Sunkai hari Barikin Soja sunyi awon gaba da garken Shanu

KARANTA: Amfanin Shan Rake Ga Mata Masu Juna Biyu


Hukumar ta JAMB tace, daliban da suka rubuta jarabawar a cibiyoyi sama da 720 a shekarar 2021 zasu iya duba sakamakon su ta wayar hannu.


A zantawar sa da manema labarai mai magana da yawun hukumar ta JAMB Dr. Fabian Banjamin ya sanar da hakan a ranar Juma'a.


Fabian ya shawarci kowane dalibi da ya duba sakamakon sa ta hanyar tura UTMERESULUT zuwa 55019 ta hanyar wayar hannu domin samun lambar sirri da rijistar UTME ta hukumar. 

Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post