Jami'an ‘yan sandan Najeriya reshen jihar Kaduna sun tabbatar da sace mutane 12 da wasu 'yan bindiga suka yi a garin Kachia da ke jihar Kaduna.
KARANTA: 'Yan Bindiga Sunkai hari Barikin Soja sunyi awon gaba da garken Shanu
KARANTA: Siffofin Da Suke Hana A Auri Mace
KARANTA: Illolin kallon fina-finan batsa
A cewar sa mai magana da yawun rundunar a jihar ASP Muhammed Jalige ya tabbatar da sace mutanen yayin zantawa da jaridar Vanguard.
Ya ce ''A ranar 23 ga watan Yuni, rundunar tasu ta samu wani rahoto mara dadi daga Kachia, cewa da daddare wasu ‘yan bindiga da ba a san ko su waye ba, dauke da muggan makamai suka mamaye mahadar Awon / Mothercat a karamar hukumar inda suka fara harbin kan mai uwa da wabi.
Ya ce, da samun wannan bayanin, hadin guiwar 'yan sanda da sojoji da kuma 'yan banga suka durfafi wajen da nufin tunkarar yan bindigar, amma sai suka tarar sun yi wa mutane hudu rauni, yayin da kuma suka kashe wani mai suna Hamisu Mikailu, mai shekaru 40 a duniya.
Ya ce sun kuma yi awon gaba da mutane 12, yayin da su kuma wadanda aka raunata ke ci gaba da karbar magani a asibiti.