Yadda 'yan kungiyar Hakika su 3 suka yiwa matar aure ciki a Katsina


Rundunar ‘yan sanda reshen jihar Katsina ta ce sun cafke wasu ‘yan kungiyar Darika ta Islama su uku da hadin baki tare da yin lalata da wata matar aure da sunan wai su shigar da ita cikin mazhabar su.


KARANTA: Yan Bindiga Sunyi garkuwa da dalibai fiye da 1,000 a arewacin Najeriy


KARANTA: Wani Mutum Ya Mutu Yayin Da Yake Jima'i Da Matar Abokinsa


Ana zargin kungiyar ta Darika da daukar ma'aikata tare da shigar da su cikin koyarwar ta su wacce ta yi kama da ta Boko Haram. A rahoton jaridar SaharaReporters


Wasu daga cikin ayyukan kungiyar da ake zargi sun hada da rashin yin sallolin farilla guda biyar da musulmai suke yi a kullum, sai kuma kin yin azumin Ramadana, da gabatar da fasikanci, da zina, da dai sauran su.


A cewar 'yan sanda, rikicin ya faro ne lokacin da mijin matar, Isiyaku wanda ya kasance a Legas sama da shekara guda yana sana'a, ya koma kauyensu na Wardanga da ke cikin Karamar Hukumar Bakori ta Jihar Katsina sai ya tarar da matarsa jaririya 'yar wata hudu.


Isiyaku, wanda ya bar matarsa, Zainab Ahmed a hannun iyayenta a kauyen Unguwar Dantalle, Tandama, dake karamar hukumar Danja da ke jihar ta Katsina ya gano cewa ta samu cikin ne bayan da wasu daga cikin membobin kungiyar su uku daga wannan kauye suka yaudare ta kuma suka yi lalata da ita.


Daga nan ya garzaya zuwa ofishin 'yan sanda na Danja ya kai rahoton lamarin ga 'yan sanda.


A yayin gudanar da binciken, Zainab Ahmed ta furta cewa ta nuna sha'awar shiga kungiyar, kuma sun fada mata cewa tsarin shiga  ya hada da yin lalata(Zina) wanda ta yarda da hakan.


“Na gaya musu cewa ina son shiga darikar sukace daya daga cikin sharuddan shiga darikar ya kunshi yin Zina da ita. Na amince kuma su ukun kowane sai da ya kwanta dani, sannan suka fara shigar da ni cikin kungiyar, ”in ji Zainab.


Sanarwar 'yan sandan ta ce, "Hakazalika, wani mai suna Abdullahi Isiyaku ɗan shekara 30 daga ƙauyen Wardanga da ke ƙaramar hukumar Bakori ta jihar Katsina ya ba da rahoto a ofishin 'yan sanda na Danja a ranar 17 ga Yuni, 2021, cewa wani lokaci a cikin Janairu 2020, ya tafi Legas don neman abinci ya kuma bar matarsa, Zainab Ahmed, mai shekaru 20 karkashin kulawar iyayenta a kauyen Unguwar Dantalle na yankin Tandama a karamar hukumar Danja ta jihar Katsina.


“Duk da haka, lokacin da ya dawo a farkon watan Yuni, ya hadu da matarsa tare da jaririya 'yar wata hudu da haihuwa. A yayin gudanar da bincike, matar ta bayyana cewa wasu mutane uku da ake zargi da yi wa fyade ne wadanda suka hada baki da ita suka ruda ta zuwa wani sabon Mazhabar Musulunci da ake kira 'Hakika'.


"Wadanda ake zargin - Tukur Dan-Azumi,  mai shekaru 19, Abubakar Yahuza, mai shekaru, Rufa'i Saosi, 27 duk a Unguwar Dantalle da ke yankin Tandama a yankin Danja."

KARANTA: Siffofin Da Suke Hana A Auri Mace

Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post