A jihar Zamfara dake arewa maso yammacin Najeriya rundunar ‘yan sandan jihar ta tabbatar da mutuwar jami’anta guda hudu.
KARANTA: Mutumin Dake Auren Mata 39 Ya Mutu
Sashen Hausa na BBC ya rawaito cewa lamarin ya faru ne a yayin wata arangama da ‘yan bindiga lokacin da suke aikin sintiri a yankin Rini cikin karamar hukumar Bakura.
Haka kuma ‘yan bindigar sun kai farmaki kauyukan Tataka da Takalmawa a karamar hukumar Zurmi inda ake fargabar fiye da mutum 20 sun mutu tare da kwashe ɗumbin dukiya a karshen makon da ya wuce .
A yan kwanakinna dai Hare-haren 'yan bindiga sun dawo sosai a jihar Zamfara.
Tags:
Labaran Duniya