Wani Mutum Ya Mutu Yayin Da Yake tsakiyar Jima'i Da Matar Abokinsa A jihar Delta
KARANTA: Yadda Ƴan bindiga suka kashe ƴan sanda huɗu a jihar Zamfara
KARANTA: Jiragen Yaki Na Sojoji Sun Kashe Sama da Shanu 1,000 A Nasarawa
KARANTA: Mutumin Dake Auren Mata 39 Ya Mutu
Wani shahararren mai sayar da naman daji a Ogharefe mai suna Mista Victor, wanda aka fi sani da Pay Cash ya mutu a yayin da yake saduwa da tsohuwar matar abokinsa mai suna Julie a Oghara, Jihar Delta.
A cewar wani rahoto, marigayin ya je gidan matar ne don yin lalata da ita, amma ya mutu a yayin hakan.
Wata majiya ta bayyana cewa Julie batada aure kuma tsohon mijinta babban aminin marigayin ne.
Jaridar Sahara Reporters sun rawaito cewa, an samu labarin cewa tsohon mijin na Julie ya nemi taimakon Victor don taimaka masa ya roki matar sa don sasanta rashin jituwar da ke tsakanin su, wanda ya haifar da rabuwar su.
Majiyar ta kara da cewa "Julie da tsohon mijin nata sun yi fada a wani lokaci da ya gabata lokacin da ya gano cewa mijinta na soyayya da Julie."