Tsagerun Neja Delta sun lashi takobin za su kashe Fulanin 10 ga duk rayuwar wanda aka kashe a Delta.
KARANTA: Mutumin Dake Auren Mata 39 Ya Mutu
KARANTA: Gwamnatin Zamfara Ta Dakatar Da Sarkin Zurmi Kan Zargin Alaka Da 'Yan Ta'adda
KARANTA: Buhari Yayi Magana Kan Shirye-shiryensa Bayan Ya Sauka Daga Mulki A 2023
Wata kungiyar tsagerun Neja Delta, wacce aka fi sani da (MEND), ta sha alwashin kaddamar da abin da ta kira mummunan ramuwar gayya ga kungiyar 'Fulani' wacce tayi barazanar mamayewa da jefa bam a birnin Asaba, babban birnin jihar da kuma Agbor. Kamar yadda shafin jaridar Sahara Reporters suka bayyana.
Fulanin, wadanda suka dauki alhakin gobarar da ta lakume hadaddiyar sakatariyar gwamnatin tarayya da ke kan titin Okpanam dake garin na Asaba, a ranar Lahadin da ta gabata ta fitar da wata wasika dauke da barazanar mamayewa da jefa bam a babban birnin jihar, Asaba da Agbor, hedkwatar Karamar hukumar Ika ta kudu a jihar
Tsagerun Neja Delta Tife Owolabi
Kungiyar ta ba Gwamna Ifeanyi Okowa awanni 72 da ya janye matsayinsa da goyon bayansa game da dokar hana kiwo a fili, wanda gwamnonin Kudancin suka yi hadin gwiwa da shi a yayin taron da suka gudanar a watan Mayu wanda Okowa ya dauki nauyin gudanarwa a gidan Gwamnati, Asaba.
Barazanar ta haifar da tsoro a tsakanin mazauna jihar Delta.