Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya isa Maiduguri babban birnin jihar Borno
Shugaban Ya samu tarbar gwamnan jihar na Borno Babagana Umara Zulum da wasu daga cikin manyan sojojin Najeriya da ke jihar.
A yayin ziyarar tasa, ana sa ran shugaban zai kaddamar da wasu ayyuka wanda gwamnatin jihar ta samar.
Sannan kuma shugaban zai kaddamar da kashi na farko na gidaje 10,000 da gwamnatinsa za ta gina domin sake tsugunar da 'yan gudun hijira wanda 'yan kungiyar Boko Haram suka kora daga gidajensu.
Tags:
Labaran Duniya