wadannan wasu shawar-wari ne da likitoci suka baiwa Mata masu dauke da juna biyu da kuma masu goyon ciki, da fatan zaku kula da su da kyau.
KARANTA: Hadin Matse Gaba Da Karin Dandanon Jima'i
KARANTA: Siffofin Da Suke Hana A Auri Mace
KARANTA: Ladan Da Mace Take Samu A Wajen Mijinta Bayan Tayi Aure
Wadannan shawarwari da likitocin suka bada sune Kamar haka:
1. Ki baiwa abinda ke cikin ki kula matuka, saboda kisami lafiya da kubuta, ke da abinda ke cikin ki.
2. ki dinga cin abinci sosai, irin wanda yake gina jiki, ta yanda zaki sami lafiya, da d'an dake cikin naki.
3. Ki dinga cin kayan mar-mari, kaman su kwad'on rama ko latas da makamantansu a kowace rana.
4. Ki dinga shan kaman kofi hudu na madara, ko nono a kowace rana.
5. Kada ki dinga yawan Shan Shayi mara madara, ko Nescafe, ko cin albasa, ko cin yaji a abinci,
6. Kada ki dinga shan magani, ba tare da shawartan likita ba, saboda hakan ze cutar da yaron, kai yana temakawa wajensa Yaron Muni.
7. Yanada kyau a rage saduwa da Iyali, lokacin da cikin yake wata uku, da kuma watan karshe na haihuwa, yawan aikata hakan yana tasiri ga lafiyarki da ta Yaron.
Sannan saduwa da mace lokacin da take cikin jinin haihuwa yanada cutarwa ga mace, saboda hakane musulunci ya haramtashi.
8. Rashin yin barci da wuri, ze sanya maki damuwa, saboda haka dolene kiyi barci na Awa tara a kowace rana, a tsawon lokacin goyon cikin.
9. Kada ki dinga yin aiki me wahala da d'aga abubuwa masu nauyi, domin hakan ze Iya samar da matsala ga cikin.
10. Ki lazimci Natsuwa, da rashin yin fushi, sakamakon wasu matsaloli na gida, ko na Y'an Uwa, saboda ki samu kwanciyan hankali, ana buk'atan hakan dan cikin yatafi yanda akeso, batare da wata matsala ba.
11. Kada ki dinga ziyartan marasa lafiya, masu dauke da ciwon daza'a iya kamuwa dashi, don ze zama hatsari agareki da kuma danki.
12. Kada ki dinga sanya tufafi masu matse jiki, ko daure ciki da k'arfi tsawon lokacin goyon cikin, dan yin hakan ze saki gajiya, da shan wahala wajen yin numfashi.
13. Kada ki dinga sanya takalma masu tsawo, wato masu dogon k'wauri dan ze sabbaba rashin walawa a gab'ubb'an jikinki, wanda hakan ze samaki ciwon baya.
14. Dolene ki dinga yawan ziyartan likita akai-akai, tsawon lokacin goyon cikin, Sau d'aya cikin kowani wata cikin wata shida na farko, da kuma sau d'aya cikin kowani sati biyu, a watana bakwai da na takwas, da kuma sau daya cikin kowani sati, a watana tara har zuwa lokacin haihuwa.
15. Ki dinga yin gwajin jini da na fitsari, lokaci zuwa lokaci saboda ki tabbatar cewa: jikinki baya dauke da wani ciwo da yaron ze iya kamuwa dashi, kaman ciwon sukari da makamantansu.
16. Dolene ki dinga yin wanka a kowace rana, a duk lokacin tsawon goyon ciki, da lokacin shayarwa, dan ki kare lafiyarki, da na yaronki. Insha Allahu.
17. Ki dinga kula da mamanki, tun daga wata na biyar da samun cikin, saboda shayar da danki mama na asali.
18. Ki dinga tafiya da k'afa a kowace rana, gwargwadon iyawarki, hakan ze kyautata maki jinin jiki lokaci zuwa lokaci, ya zama abinci ga danki, kuma ya sauwak'e maki haihuwa.
19. Anason haihuwa a asibiti, saboda samun kula da Uwa da danta, kuma babu laifi ta haihu a gida idan ta shawarci likita ya tabbatar mata da cewa duk abinda ya shafeta da d'anta yana tafiya daidai, kuma ya nisantarda samun wata matsala, kuma yazama akwai abubuwan da suka shafi samun lafiya a gida.
20. Ki dinga yin ayyukan gida, ke da kanki bayan kin haihu da y'an kwana kadan, domin hakan zesa mahaifarki ta koma yanda take ada, ya karfafa maki gab'ob'in jiki, kuma ya hana …..ciki da k'irji, kuma ya temaka wajen samar da mama ga jariri.
Allah nake roko da ya sauwak'e maki wahalhalun haihuwa kuma ya baki zurriyya.