Wannan hadin na maganin maleria ne wanda aka fi sani da cizon Sauro, kuma idan aka hada akayi amfani dashi za'a Sami waraka insha Allah.
KARANTA: Indai matsala sanyin mara ne to daga yau tazo karshe
KARANTA: Yadda Zaku Magance Matsalar Kansar Nono Da Ganyen Gwaiba
Assalamu Alaikum Warahmatullah wabarakatuh, 'yan uwa barkanmu da war haka da fatan muna cikin koshin lafiya, Allah yasa haka amen.
A yau ma kamar kullum na kawo muku wata hanya na hada maganin zazzabin cizon Sauro, wanda a wannan lokaci yake addabar jama'a, insha Allahu wannan hanya tana magance wannan ciwon cikin kankanin lokaci da yardar Allah, kuma a samu sauki.
Akwai alamomi da mutum zai gane ya kamu da Zazzabin cizon sauro sune kamar haka.
KARANTA: Yadda Zaku Magance Matsalar Kansar Nono Da Ganyen Gwaiba
- Ciwon kai
- Rashin jin da]in cin abinci
- Kasala
- Amai
- Gudawa
- Tafiyar ruwa (Convulsion)
- Alamun rashin isasshen jini
- Kakkarwa
- Ramewa
- Suma
-Zafin jiki, Da sauransu.
Hanyar da za'a magance wannan cuta shine.
KARANTA: Indai matsala sanyin mara ne to daga yau tazo karshe
Za'a samu wannan abubuwan Kamar haka:
1. Bawon Abarba
2. Lemon tsami
3 ruwa
Yadda Za'a hada wannan maganin shine Kamar haka:
Za'a samu bawon Abarba daidai misali lemon tsami rabi idan yana da girma idan kuma bashi da sai a saka guda daya, ruwa Kamar kofi 4.
Da farko za'a wanke bawon sannan a zuba a tukunya a yayyanka lemon tsamin a zuba harda bawon a ciki, sannan a dafa na Kamar tsawon minti 30.
Bayan an sauke sai a zuba a filas, a rika shan kofi daya har sau 4 a rana ga babba mutum
Yaro daga shekara 7 zuwa 12 zai sha rabin kofi sau 2 a rana.
Tsawon kwana 3 insha Allahu za'a samu sauki.
Abin sadaqa ayiwa Annabi sallallahu Alaihi wasallam Salati.
KARANTA: Hadin Matse Gaba Da Karin Dandanon Jima'i
Idan ka karanta ka tura zuwa yan uwa domin su samu