Fiye da Mayaƙan ƙungiyar ISWAP 50 ne rundunar sojan Najeriya ta ce ta kashe a Jihar Borno a ranar Laraba.
KARANTA: Ku Kashe Duk Wani Wanda Aka Kama Da Bindiga, Gwamna Matawalle
KARANTA: Mayakan ISWAP Sun Mamaye Al'ummar Borno, Sun Afkawa Sojojin Najeriya
KARANTA: An Cafke Wani Mutum A Sakamakon Yiwa 'Ya'yansa Mata Fyade
A cewar sa Mai magana da yawun rundunar, Birgediya Janar Yerima Mohammed, ya fada cewa dakarunsu sun yi nasarar kashe 'yan bindigar ne yayin da suka yi yunƙurin kai hari a Ƙaramar Hukumar Damboa da ke Borno.
Dakarun rundunar musamman wadda aka sani da Operation Hadin Kai ne suka samu nasarorin tare da taimakon sojojin sama, a cewarsa.
"'Yan ta'addan sun kai hari garin da dukkan ƙarfinsu da manyan motocin su masu ɗauke da bindigogi guda 12 da makaman harbo jirgi da babura da kuma ababen fashewa," a cewarsa cikin wata sanarwa.
"Jajirtattun sojojin sun daƙile harin sannan suka lalata motoci masu silke tare da kashe 'yan ta'addan ISWAP su kimanin 50, abin da ya jawo wasu daga cikin 'yan bindigar suka tsere sakamakon luguden wuta daga sojojin sama."
Da yake mayar da martani kan lamarin, Babban Hafsan Sojan Ƙasa Manjo Janar