Ku Kashe Duk Wani Wanda Aka Kama Da Bindiga, Gwamna Matawalle




Gwamnan Jihar Zamfara Matawalle da ke arewacin Najeriya ya sake bai wa jami'an tsaro damar harbin duk wani mutumin da aka gani ɗauke da bindiga ƙirar AK-47 ko kuma wani makami.





Gwamnan ya jadadda umarnin da Shugaba Buhari ya bayar ne tun a watan Maris, yana mai cewa jami'an tsaro da waɗanda doka ta bai wa dama ne kaɗai za su riƙe makami idan basu ba duk wanda aka gani da wani makami a harbe shi kawai.


Wannan umarnin ba ya rasa nasaba da yadda jihar take fama da hare-haren 'yan fashi kusan a kullum, inda suke kashe mutane da kama wasu don karɓar kuɗin fansa.


"'Yan sandan Zamfara da sauran jami'an tsaro su tabbatar sun aiwatar da umarnin shugaban ƙasa na harbe 'yan fashi nan take ko kuma wasu mutane da aka gani ɗauke da bindigar AK-47 ko wani makami," a cewar gwamnan cikin wani saƙon sa da ya wallafa a Twitter.


A baya dai, gwamantin Matawalle ta sha tabbatar da cewa shirinta na sasantawa da 'yan fashin na taimakawa wajen raguwar hare-haren.

Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post