Sergio Ramos mai shekaru 35, mai tsaron bayan kungiyar Sifaniya, na duba kungiyar da ya kamata ya koma buga wasa, bayan da Bayern Munich, Manchester city da Paris St Germain suke zawarcin dan wasan. (ESPN)
Tottenham hustpor bata so dan wasa Gareth Bale ya cigaba da taka leda a kungiyar wanda ya buga mata wasa a matsayin aro a kakar da ta gabata, inda dan wasan mai shekara 31 zai koma kungiyar sa ta Real Madrid, wadda saura kaka daya kwantiraginsa ya kare a kungiyar.
Rennes ta ce ba wata kungiya da ta taya dan kwallon tawagar Faransa, Eduardo Camavinga a wajenta, duk da ana alakanta dan wasan mai shekara 18 da cewar zai koma taka leda Manchester United ko kuma a Paris St-Germain. (Metro)
Roma ta kusan kulla yarjejeniyar daukar mai tsaron ragar Portugal, Rui Patricio, mai shekara 33, daga Wolves.