Jirgin sama guda biyu na soja sun kashe shanu sama da 1,000 a wasu hare-hare da dama da aka kai wa mazauna Fulani a kananan hukumomin Keana da Doma na jihar Nasarawa
An kai hare-haren ne tsakanin ranakun Alhamis da Lahadi ...
KARANTA: Tsagerun Neja Delta Sun Lashi Takobin Kashe Fulani 10 Fansa Ga Duk Wanda Suka Kashe A Jihar
KARANTA: Mutumin Dake Auren Mata 39 Ya Mutu
KARANTA: Buhari Yayi Magana Kan Shirye-shiryensa Bayan Ya Sauka Daga Mulki A 2023
Shugabannin Fulani da wasu daga cikin wadanda abin ya shafa sun shaida wa Jaridar Daily Trust cewa an fara kai hare-haren ne tsakanin ranar Alhamis, 10 ga Yuni da Lahadi, 13 ga Yuni.
Wasu matasa Fulani makiyaya da ke kula da shanun sun samu raunuka yayin da shanu sama da 500 da suka bi ta cikin makwabtan jihar Binuwai ba a gano su ba har yanzu, in ji wadanda lamarin ya rutsa da su.
Wasu majiyoyi sun ce an kashe daruruwan shanu a yankin Giza na Karamar Hukumar Keana a kan dalilin cewa aikin da sojoji suka yi shi ne don fatattakar ‘yan fashi daga yankunan.
An tattaro cewa aikin na ranar Lahadi ya dauki tsawon awanni uku kuma ya haifar da rikici a yankunan yayin da manoma da Fulani makiyaya suka kaurace wa gidajensu saboda tsoron kada a kashe su.
Daga birnin Lafiya wani ya shaidawa sashin Jaridar Daily Trust cewa, an kashe shanu sama da 1000 yayin da wasu da dama suka ji rauni.
Rahotanni sun ce harin da jiragen yakin rundunar Sojin saman na Najeriya suka kai ya kwashe tsawon awanni uku yana faruwa, yayin da Al'ummar yankin suka tsere sakamakon faruwar wannan al'amari.