Shirye-shiryen bikin auren dan Shugaba Muhammadu Buhari, Yusuf Buhari, an fara shi sosai.
A ranar Lahadi, tawagar Shugaban kasar ta ziyarci fadar Sarkin Kano inda aka yi magana game da bikin auren.
Gwamnan jihar Jigawa, Abubakar Badaru, ya jagoranci tawagar shugaban zuwa fadar mai martaba Sarkin Kano tare da sauran manyan jami’an gwamnati.
An tattaro cewa Yusuf, dan da Shugaba Buhari ya haifa ya hadu da masoyiyar tasa, Zarah Ado Bayero, a kasar Ingila inda dukkan su suka yi karatun digiri na biyu.
Anan ga abubuwa masu ban sha'awa da ya kamata ku sani game da 'surukar' shugaban kasa:
Yar Sarkin Bichi
Zarah Ado Bayero ’yar shekara 19 ce ga Sarkin Bichi, Alhaji Nasir Ado Bayero, wanda shi ne na hudu ga marigayi Sarkin Kano, Alhaji Ado Bayero. Mahaifinta, banda kasancewarsa Sarki, shine ciyaman a kamfanin 9mobile. Shi ne ɗan fari da aka haifa a gidan masarautar Kano da aka fi sani da Gidan Dabo.
Ya kasance hakimin kananan hukumomin Fagge, Tarauni da Nassarawa kafin gwamnatin Gwamnatin Abdullahi Ganduje ta nada shi Sarki mai daraja ta daya.
Alakar su da Sokoto
Yayin da mahaifiyar Zarah, Farida Imam, ‘yar shahararren Malami a Kano ne, Mal Abubakar Imam (Imamu Galandanci), tsohon Babban Darakta a Bankin Afrika, Sarkin Musulmi, Muhammad Sa'ad Abubakar III, ya auri kanwar Farida.
Ilimi
Zarah, ita ce 'ya ta biyu ga Sarki kuma a fannin ilimi ta karanci fannin gine-gine a Ingila.
Tags:
Shirye-Shirye