Garuruwa da dama ne wanda 'yan fashin suka kone a yayin harin da suka kai a cewar wani dan majalisa mai wakiltar yankin.
KARANTA: Wani Mutum Daya Bata Sama Da Shekaru 60 Ya Bayyana A Garin Kano
KARANTA: Dalilai biyar da suka tabbatar da mutuwar Abubakar Shekau
KARANTA: Yadda Mutum 13 Suka Rasa Rayukan Su A Hadarin Jirgin Ruwa A Sokoto
Rahotanni daga jihar Zamfara a arewa maso yammacin Najeriya na nuna cewa 'yan fashin daji sun sace wasu mata kimanin su 60 a cikin wani farmaki da suka kai kan wasu kauyuka a ranar Talata. Kamar yadda shafin gidan Radio Bbc Hausa suka rawaito.
A cewar wani ɗan majalisar wakilai dake daga yankin, ya bayyana cewa an sace matan ne daga kauyen Manawa yayin da aka kashe mutane hudu a kauyukan Malele da Randa a Karamar Hukumar Maru.