Antisa keyar tsohon shugaban Kwamitin binciken tallafin mai a majilasar wakilan Najeriya Faruq Lawan kurkukun Kuje
KARANTA: Ƴan bindiga sun tilasta wa mutane guduwa daga wasu garuruwan jihar Neja
KARANTA: Siffofin Da Suke Hana A Auri Mace
KARANTA: Illolin kallon fina-finan batsa
Tsohon shugaban kwamitin binciken tallafin mai a majalisar wakilan Najeriya an aike dashi shiga gidan yarin Kuje a Abuja bayan an yanke masa hukunci a ranar Talata, kamar yadda shafin Jaridar Bbc Hausa ta ruwaito.
Jaridar ta Kara da cewa ba tare da ɓata lokaci ba aka tafi da Farouk Lawan gidan yari na Kuje bayan da kotu ta zartar masa da hukuncin ɗaurin shekara bakwai da zaiyi a gidan yarin.
Wata majiya daga jaridar Daily Trust ta ambato cewa Faruq Lawan din zai ci gaba da zama a gidan yarin har zuwa cikar wa’adin da aka dibar masa na shekaru 7. Sai idan kuma ya ɗaukaka ƙara kuma ya yi nasara wanda zai sa a sake shi.
Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja a ranar Talata da ta gabata ta sami Farouk Lawan ne da laifin karbar cin hanci na kudi dala 500,000 a wurin shararren dan kasuwa Femi Odetola domin wanke kamfaninsa daga badaƙalar tallafin mai.