Dalilai biyar da suka tabbatar da mutuwar Abubakar Shekau


Tun bayan makonni biyu da suka gabata ake samun labarin dake ta yawo cewa an kashe shugaban Boko Haram Abubakar Shekau. 


KARANTA: Yadda Mutum 13 Suka Rasa Rayukan Su A Hadarin Jirgin Ruwa A Sokoto

KARANTA: Mun Kashe 'Yan ISWAP Su 50, Inji Sojojin Najeriya

KARANTA: Cutar Korona Tana Cigaba Da Kashe Mutane A Najeriya


Kuma a cikin wannan satin an ƙara samun wasu dalilai da ke ƙara tabbatar da labaran farko da ke iƙirarin mutuwar tasa.


Sai dai ƙungiyar Boko Haram da gwamnatin Najeriya ba su tabbatar da mutuwar Abubakar Shekau ba wanda sojin Najeriya da na Amurka suke nema ruwa a jallo.


Shafin Hausa na BBC ta tattauna da masanin harkokin tsaro kuma jami'i a Cibiyar Bincike ta Tony Blair da ke Burtaniya, Barrister Bulama Bukarti inda ya bayyana manyan dalilai guda biyar da ke tabbatar da shugaban Boko Haram Abubakar Shekau ya mutu.


Ga Dalilan Guda Biyar Da Masanin Ya Bayyana

Masanin ya ce dalili na farko shi ne yadda aka fara samun labarin da ke iƙirarin cewa an kashe Shekau.


Kuma labarin ya fara fitowa ne daga wasu jaridun Najeriya da suke da kusanci da alaƙa ta kusa da kusa da sojoji da kuma jami'an tsaron Najeriya.


A cikin labarin da jaridun suka wallafa sun nuna yadda jami'an tsaro suka yi kutse a wayoyin manyan kwamandojin ISWAP inda suka ji suna labarin yadda suka je suka kashe Shekau.


Masanin ya ce dalili na biyu shi ne tabbatar da labarin da wasu jaridu masu kusanci da Boko Haram ɓangaren Shekau da kuma ISWAP suka yi.


Ya ce sun yi labarai a kan yadda suka tattauna da majiyoyinsu na ɓangarorin ƙungoyoyin biyu da ke hamayya da juna.


Kuma jaridun sun ce majiyoyin sun tabbatar masu da cewa Shekau ya mutu.


Dalili na uku a cewar masanin shi ne majiyoyi daga mutanen yankin arewa maso gabashi da suka tabbatar da mutuwar shugaban na Boko Haram.


Ya ce rahotanni da dama daga mutanen da ke yankin Borno da Tafkin Chadi da suke da majiyoyi daga ƙungiyar Boko Haram sun tabbatar da cewa Shekau ya mutu.


Barista Bukarti ya ce wani babban dalili shi ne yadda aka ji shiru ba wani sabon bidiyo daga shugaban na Boko Haram.


Ya ce har yanzu ba a ga Shekau bai fito ya musanta ba domin a baya yakan fito ya musana ikirarin cewa an kashe shi.


Duk aka yi wani labari da ya ja hankali game da shugaban na Boko Haram ko kuma ita ƙungiyar yakan fito ya ƙaryata.


Masanin ya ce an taɓa fito da wani bidiyo da ke nuna Shekau kamar yana kuka amma nan take ya fito ya yi gaggawar musantawa inda ya ce tsohon bidiyo ne.


Yanzu kuma an yi tsawon mako biyu amma har yau ba labarin Shekau, "kuma idan da yana raye da ya fito yana ɓaɓatu," in ji Bukarti.


Masanin ya ce hujja ta biyar da ta fi karfi kawo yanzu ita ce ISWAP da ta fito ta tabbatar da mutuwar Shekau.


Ya ce a ranar Juma'a ISWAP ta fitar da sanarwa inda a ciki suke tabbatar da cewa sun kashe Shekau tare da ba da labarin yadda suka halaka shi.


A cewar, cikin sanarwar sun nuna cewa Shekau ne ya kashe kansa ta hanyar tayar da bom da ke jikinsa.


Barista Bukarti wanda ya daɗe yana bincike kan ayyukan Boko Haram ya ce "wadannan hujjoji za su iya tabbatar da cewa Shekau ya mutu.


Kuma ya ƙara da cewa mayakan ISWAP sun ce suna ci gaba da yaƙi da kwamandojin Shekau bayan sun kashe shugabansu.


Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post