A hare-haren da masu garkuwa da mutane suke kaiwa a arewacin Najeriya sun sace dalibai sama da 1,000 da kuma malamai a makarantun su dake fadin arewacin tunda ga watan Disamaban zuwa yanzu.
KARANTA: Boko Haram sunyi Yunkurin Karbe sansanin Sojin Sama da ke Kaduna
KARANTA: JAMB ta saki sakamakon jarabawar UTME ta wannan shekarar
Matsalar garkuwa da mutane ta ta’azzara mawuyacin halin da fannin ilimi a kasar yake ciki, inda da ma Najeriya ce kasar da aka fi samun yawan kananan yaran da ba sa zuwa makaranta a fadin duniya. Musamman a arewacin Najeriya, wanda hukumar majalisar Dinkin Duniya ta bada rahoto a kai.
Sai dai kuma duk da hakan, su ma sauran yaran da ake ganin cewa suna zuwa makarantun lamarin ya na nema ya gagara a dalilin barazana da ilimin yake fuskanta na yawaitar kai hare-hare a makarantu da sace daliban ayi garkuwa dasu domin neman kudin fansa.
A bisa binkicen da Duniyarilimi tayi kan wannan sace dalibai da ake zuwa ayi a makarantun su, tundaga watan Disamba na shekarar 2020 kawo yanzu anyi garkuwa da dalibai da malaman su sama da 1,000 a makarantun nasu.
KARANTA: Yan sanda sun tabbatar da sace mutane 12 a jihar Kaduna