Ƴan bindiga sun tilasta wa mutane guduwa daga wasu garuruwan jihar Neja

 


Mazauna wasu yankuna a jihar Neja dake yankin arewacin Najeriya suna cigaba da tserewa daga yankunan su zuwa inda zasu tsira a sakamakon hare-haren 'yan bindiga. 


KARANTA: Yan Bindiga Sun Saki Hotunan Dalibai, Da Malamai Da Suka Sace Daga Makarantar Kebbi

KARANTA: Dan wasan Najeriya Shehu Abdullahi ya auri 'yar film Naja'atu 'yar Baba

KARANTA:Sama Da Dalibai Da Malamai 100 Ne aka Sace A Makaranta A Jihar Kebbi


Mutanen garin Galadiman Kogo na karamar hukumar Shiroro sun tsere zuwa wasu garuruwa, bisa tsoron hare-haren 'yan bindiga bayan da aka janye wata tawagar jami'an tsaron da ke gudanar da sintiri a garin.


Kaurace wa garin da jama'arsa suka yi dai ya haddasa asara mai dimbin yawa ga manoma da masu gudanar da sauran sana'o'i.


Sai dai kuma gwamnnatin jihar ta Neja, ta ce ana shirin kaddamar da wasu matakan tsaro masu inganci na dindindin a yankin da ma sauran sassan jihar da ke fama da matsalar tsaro.


Yanzu haka dai illahirin garin na Galadiman Kogo a yankin karamar hukumar Shiroro ta jihar Neja, ya koma kusan kamar kufai, a cewar wani mutumin garin mai suna Mubarak Danladi wanda jaridar bbc Hausa ta zanta dashi yace:



"Mun gudu mun tsere, wasu sun tafi garuruwa makofta, wasu kuma birnin Minna suka gudu, da sauran wurare da dama, saboda barayin sun ajiye doka duk lokacin da jami'an tsaro zasu bar garin sai sun kawo hari musamman a Galadiman Kogo, su na zuwa wai mu yi sulhu da su, mu kuma mun ki amincewa da hakan shi ya sa wannan karon muka tsere daga garin," in ji shi.
Mubarak ya kara da cewa sun kwashe shekaru uku suna fama da wannan matsala ta hare-haren 'yan bindiga a yankin, har sai da aka kai masu jami'an tsaro a 'yan watannin da suka gabata, sannan suka dan sami sauki.


Sannan barayin su na fasa shaguna su na sace kayan abinci da duk abin da ya ke da daraja kama daga na kayan abinci zuwa na bukatun yau da kullum.


Labarin halin da mutanen garin na Galadiman Kogo ke ciki dai, ya isa kunne gwamnatin jihar Nejar, kuma Ahmad Ibrahim Matane, sakataren gwamnatin jihar, ya ce ana kokarin kaddamar da wani shiri mai dorewa, don magance matsalar tsaron gabaki daya.


Masu sharhi kan al'amuran tsaro dai na ganin matsalar tsaro tana ci gaba da zame wa gwamnatocin jihohi wani kulli gagara kunta, domin haka, sai gwamnatin tarayya ta kara zage damtse wajen murkushe matsalar.

Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post